1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gidajen kallon kwallon kafa a Najeriya na fiskantar barazanar tashin bama-bamai

June 19, 2014

Tun bayan da aka fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Brazil ake samun tashin bama-bamai a irin wadannan gidajen kallon, wadanda har suka kai ga hallakar rayuka.

https://p.dw.com/p/1CM19
Nigeria Boko Harem Selbstmordattentat WM Public Viewing Damaturu
Hoto: picture-alliance/AP

Gasar kwallon kafa dai na da dimbin ma'abota a Najeriya ko da ko a wace nahiya ce, kuma daya daga cikin abubuwan da ke karawa wasan armashi shi ne idan ma'abota sun taru a gidan kallo guda, suna kallo cikin zumunci da walwala, suna tsokaci kan abubuwan da ke sosa musu rai dangane da wasar.

To amma yau an wayi gari ana fiskantar barazanar shudewar irin wadannan gidajen kallo saboda barazanar rashin tsaro.

Tuni ma wasu jihohin Najeriyar suka haramta irin wadannan gidajen kallon dan rage afkuwar irin wannan matsalar.

Ga dai rahotannin da muka hada kan wannan batu daga karkashin wannan shafin