1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Akufo-Addo ba zai yi tazarce ba

December 8, 2021

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya jaddada cewa zai mutunta dokokin kasarsa na yin wa'adin shugabancin sau biyu kacal, maimakon sauya kundin tsarin mulki don yin tazarce.

https://p.dw.com/p/440id
ECOWAS Westafrikanische Staaten verhängen Sanktionen gegen Mali und Guinea
Hoto: Nipah Dennis/AFP

A lokacin da yake jawabi da birnin Accra, Shugaban ya shawarci takwarorinsa na Afirka da bin wannan tafarki yayin da wasu ke sauya kundin tsarin mulkin kasarsu da nufin yin tazarce.

Akufi-Addo wanda ke jagorantar kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS ko CEDEAO ya ce tuni kungiyar ta fara aiki kan sabbin dokokin hana shugabanni yin mulki fiye da wa'adi biyu. Ana dai gainin kasar Ghana a matsayin daya daga cikin kasashen Afitrka da ke bin tafarkin demokradiyya yadda ya kamata. 

Shugaba Alpha Conde na Guinea da takwaransa na Ivory Coast Alassane Outtara dai sun sake darewa kan karagar mulki a karo uku bayan yin garanbawul ga kundin tsarin mulkin kasa, lamarin da ya haifar da munanan zanga-zanga a kasashen.