Gaza na fama da matsalolin tattalin arziki
June 2, 2015A ci gaba da ziyarar aiki zuwa yankin Gabas ta Tsakiya Minsitan harkokin wajen kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ziyarci yankin Zirin Gaza na Palasdinawa. A lokacin wannan ziyara zuwa yankin zirin Gaza na Falasdinu, Ministan harkokin wajen kasar ta Jamus, Frank-Walter Steinmeier ya gana da masunta wadanda suke rayuwa cikin yanayi na wahala. Steinmeier ya tabbatar yana sane da cewa rayuwa ba ta da sauki a yankin:
"Kun san cewa ba wannan ne karon farko da na ziyarci zirin Gaza ba, na sani tun zuwa na baya. Babu rayuwa mai inganci a zirin Gaza."
Yanzu haka akwai kimanin Falasdinawa milyan biyu da ke cikin matsanancin rayuwa. Ministan ya ziyarci garin Schedchahiya inda sojojin Isra'ila suka kwashe mako guda suna barin wuta.
Mahimmancin tallafin kasashen ketare a wannan yankin
Steinmeier yana da masaniyar cewa mutanen yankin sun dogara ne da taimakon kasashen ketare. Ministan ya gane wa idonsa yadda wannan taimako ya ke tasiri a yankin na zirin Gaza, inda a wasu wuraren ajiye kifi da aka gina wa masuntan. Ma'aikatar kula da raya kasashen ketere ta Jamus ta gina wuraren da kimanin Euro130,000. Thomas Eisenbach ya kasance daya daga cikin wadanda suka kula da aikin:
"Kafin gina wajen ajiye kifin na zamani masinta sun dogara ne da wasu hanyoyin gargajiya. Wannan aiki ya taimaka wajen samar musu da igantantattun hanyoyi. Amma duk da haka idan mutum yana tafiya a bakin ruwan zai ga yadda ake ci gaba da amfani da hanyoyin gargajiyar saboda na zamanin sun kasa."
Gudunmawar Jamus a Yankin Gabas ta Tsakiya
Nahed Fouad el-Habil ya kasance daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan shiri na Jamus, sai dai kar zuwa yanzu abin da yake samu bai taka kara ya karya ba, saboda mai wuce Euro 230 a duk wata ba. Rayuwar wadannan masinta zai ingata sosai ne kawai idan aka kara yawan wurin da aka amince a yi kamun kifi a cikin ruwan.
Frank-Walter Steinmeier ministan harkokin wajen kasar ta Jamus ya ce za su ci gaba da fafutukar ganin an bude yankin na zirin Gaza domin kasuwanci da ci-gaban al'umar.
"Muna bukatar an fitar kayyakin daga nan domin, kuma haka zai kasance ne idan aka bude iyaka."
Ranar Lahadin da ta gabata ministan harkokin wajen kasar ta Jamus Frank-Walter Steinmeier ya gana da Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila da Shugaba Reuven Rivlin, daga bisani ya kuma gana da Firaminista Rami Hamdallah na Palasdinawa a garin Ramallahinda ya bukaci duk bangarorin biyu su koma kan teburin sulhu.