Gasar cin kofin duniya na ƙwallon ƙafa a Afirka ta Kudu
May 21, 2010A halin yanzun dai makonni uku ne kacal suka rage dangane da gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya a Afirka ta Kudu a saboda haka bai zama abin mamaki ba kasancewar a wannan makon batutuwa masu nasaba da gasar da kuma tarihin wasu yankuna na nahiyar Afirka su ne suka mamaye kanun rahotannin da jaridun na Jamus suka gabatar game da nahiyar ta mu ta Afirka. A cikin nata rahoton jaridar Rheinische Post ko da yake ta fara ne da yin nuni da dubban ɗaruruwan 'yan Afirka da kan yi kasadar shigowa Turai ko ta halin-ƙaƙa a ƙoƙarin neman kyautata makomar rayuwarsu, amma kuma sai ta ce:
"A haƙiƙa dai Afirka ta Kudu mai mutane miliyan 48 ita ce babbar ƙasar da ta fi karɓar 'yan gudun hijira a nahiyar Afirka. A sakamakon wadatar da Allah Yayi mata ƙasar ta zama kamar maganaɗisu. Daga cikin 'yan gudun hijira masu neman mafakar siyasa kimanin dubu 850 da aka lissafta a sassa daban-daban na duniya a shekara ta 2008, dubu 200 sun runtuma ne zuwa Afirka ta Kudu. Alƙaluma sun nuna cewar tun bayan kawo ƙarshen mulkin wariyar jinsi a shekara ta 1994 kimanin mutane miliyan huɗu suka kutsa kai zuwa ƙasar. Wasu alƙaluman ma sun ƙiyasce adadin zai kai mutane miliyan shida. Sai dai kuma a ɗaya ɓangaren ƙasar na asarar ƙwararrun ma'aikata inda kawo yanzu likitoci kimanin dubu 10 da nes-nes kimanin dubu 50 suka juya mata baya."
Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung nuni tayi da cewar:
"Duk da ɗoki da murnar da ake yi a game da gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya da za a gudanar karo na farko a nahiyar Afirka, amma duka-duka 'yan kallo dubu 85 ne kacal ake sa ran zasu halarci wasan daga sauran ƙasashen Afirka. Kuma ko da yake akwai masu danganta wannan ƙarancin adadin da matsaloli na ƙarancin kuɗi, amma kuma akwai masu ɗora laifin kan hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA, wadda aka ce ta dage akan sayar da tikitin kallon wasannin ga 'yan Afirka ta yanar gizo, a yayinda a wasu yankunan ake sayar da su kai tsaye ga jama'a."
A nata ɓangaren jaridar Neues Deutscland tayi nazari ne akan bunƙasar tattalin arziƙin da nahiyar Afirka ke samu yanzu haka, wadda a shekarar kuɗi ta bana ake sa ran ƙasashenta zasu samun bunƙasar da ta zarce ta kashi huɗu cikin ɗari. Amma ayar tambaya a nan ita ce ko al'umar Afirka kan gani a ƙasa? Jaridar sai ta ci gaba da cewar:
"Idan dai an ɗauki ƙasar Angola ta zama abin misali to lalle kam za a iya cewa lamarin da walakin. Ƙasar wadda ita ce tafi kowace samar cinikin mai a nahiyar Afirka kuma ake sa ran zata samu bunƙasar kashi tamanin da rara cikin ɗari a shekarar kuɗi ta bana, amma fa har yau al'umar ƙasar na fama da mummunan talauci da ƙarancin muhallin zama da wutar lantarki da ma ruwan sha mai tsabta. A kuma daidai nan ne take ƙasa tana dabo dangane da bunƙasar tattalin arziƙin Afirka da ake batu kanta."
Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi