Gargadi ga masu son kai ziyara a Kirimiya
March 11, 2014Mayakan sa kai da ke da iko a yankin Kirimiya na kasar Yukren, amma kuma da ke goyon bayan Rasha, sun bayar da sanarwar dakatar da zirga zirgar jiragen sama ko dai zuwa, ko kuma ficewa daga babban filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Simferopol, da ke zama hedikwatar yankin. Sai dai kuma mayakan suka ce wannan hanin, bai shafi jiragen saman da ke jigila zuwa birnin daga birnin Moscow, hedikwatar Rasha ba.
Kamfanin dilancin labaran Faransa ya ce tuni dama mayakan sa kai din suka karbe iko da kula da sauka da tashin jiragen sama a babban filin, kana wani jirgin saman da ya taso daga Kiev, babban birnin kasar ta Yukren a wannan Talatar ma sun tilasta masa komawa zuwa Kiev din, domin sun hanashi izinin sauka.
A halin da ake ciki kuma, Majalisar Dinkin Duniya na shirye shiryen gudanar da taron gaggawa domin tattauna samar da mafita ga rikicin na Yukren, kamar yadda kakakin sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya bayyana cikin sanarwar da ya fitar daga Ban Ki Moon:
Ya ce " Ina kara nuna damuwa game da yadda lamura ke ci gaba da rikidewa a Yukren. Tun bayan barkewar rkicin ne nake ta yin kira ga bangarorin da ke cikin rikicin da su sassauta domin hana rincabewarsa, kana su zauna akan teburin sulhu domin maido da zaman lafiya da lumana. Abin takaici ne ganin cewar, sai karuwar zaman dar dar ne ake samu a Yukren. Ina yin kira ga dukkan bangarori da su kaucewa rungumar tafarkin da zai dagula matsalar.
A dai ranar Litinin (17. 03. 14) da ke tafe ne kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniya zai yi zaman, a bisa bukatar da hukumomin Yukren suka gabatar mata.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe