1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin karshe na zaben Turkiyya

Suleiman Babayo
April 15, 2017

Gangamin karshe na yakin neman zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin Turkiyya.

https://p.dw.com/p/2bI1l
Türkei Referendum
Hoto: picture alliance/dpa/M. Kappeler

Shugaba Recep Tayyip Erdogan naTurkiya ya fito lokacin gangamin karshe a yakin neman zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki, inda ya nemi ganin magoya baya sun amince da sabon kundin da gagarumin rinjaye. An yada gangamin kai tsaye ta kafofin yada labaran kasar. Sai dai masu adawa suna zargin shugaban da neman shimfida mulkin kama-karya.

Idan aka amince da gyaran kundin tsarin mulkin Turkiya za ta yi bankwana da tsarin da majalisa take da karfi sannan Firamnista yake rike da madafun iko, inda karfin iko zai koma hannun shugaban kasa. Gwamnatin kasar ta haramta wani ya wallafa sakamakon zaben kafin hukumar zabe ta bayyana a hukumance.