Ana gangamin karsahe na yakin neman zaben Turkiyya
June 22, 2018Talla
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya yana gangamin karshe na yakin neman zaben shugaban kasa a birnin Santambul. Akwai 'yan takara guda shida da ke fafata zaben ranar Lahadi.
Kuma Shugaba Erdogan ake ganin zai samu nasara yayin wannan zabe da ke tafe. A shekara ta 2017 aka gyaga ga kundin tsarin mulkin kasar ta Turkiyyya inda aka kara karfin shugaban kasa maimakon firaminista. Daukacin 'yan takara suna yunkurin karshe na jan ra'ayin masu kada kuri'a.