1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin adawa da sabbin hukumomin Yukren

March 1, 2014

Mutane fiye da dubu goma ne suka yi zanga-zanga a birnin Donestsk, yankin da henbararen shugaban kasar Yukren ke da karfin magoya baya.

https://p.dw.com/p/1BHxk
Hoto: Reuters

Masu zanga-zangar dai na tafe ne suna kiran Rasha, tare da daga tutar kasar ta Rasha, yayin da wasu ma suka fara ambaton cewa, suna masu goyon bayan kasar ta bi Rasha.

Dakaru dauke da makammai, sun karbi jagorancin filayen tashi da saukar jiragyen sama da dama na Crime, yankin dake kudancin kasar ta Yukren kuma mai goyon bayan kasar ta Rasha, yayin da sabin shugabanin na Kiev, ke cigaba da cewa wannan wani salo ne na mamaya daga Rasha.

An watsa wasu takardu dake dauke da kalaman cewa, kar a aminta da sabin hukumomin na Kiev, inda masu zanga-zangar suka ce sam bazasu yarda ba.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Zainab Mohamed Aboubakar