Mahmoud Abbas ya kai ziyara yankin Yahudawa
December 29, 2021Shugaban Gwamnatin Falasdinawa Mahmoud Abbas ya gana da ministan tsaron Yahudawa Benny Gantz, a wata ziyarar ta ba-zata da ta shiga kundin tarihi, inda majiyar ma'aikatar tsaron Isra'ila ta ce, sun tattauna batutuwan da suka danganci tsaro da yadda za a inganta zamantakewa a tsakanin kasashen biyu. Ziyarar na daya daga cikin jerin ganawar da manyan jami'an Isra'ilan ke yi da jagoran Falasdinawan a baya-bayan nan.
Duk da cewa sabon firaiministan Isra'ila Naftali Bennett, ya riga ya kawar da batun tattaunawar zaman lafiya a tsakaninsu bisa kin amincewa da 'yancin gashin kan makwabtansa, ya ce, yana son ganin an shawo kan takun saka da Falasdinawa tare da inganta yanayin rayuwar al’ummar da ke zaune a yankin yammancin Kogin Jordan da Isra’ilan ta mamaye.