1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Putin da Poroschenko a Normandy

June 6, 2014

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya tattauna da sabon takwaran aikinsa na Ukraine Petro Poroschenko a karon farko tun bayan da aka zabeshi shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/1CE4w
Hoto: Reuters/Guido Bergman/Bundesregierung

Hukumomin Paris sun bayyana cewa shugabannin biyu su shafe mintuna 15 suna musayar yawu tsakaninsu a Normandy, a kan hanyoyin warware rikicin da Ukraine ke fama da shi. Da ma dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta shiga tsakanin bangarorin biyu da nufin basu damar fahimtar juna a bukukuwan cika shekarau 70 da kwato Normandy daga hannun sojojin Hitler a zamanin yakin duniya na biyu.

Tun da farko dai gwamnatin Faransa ta yi fatan ganin an dasa tubalin musayar yawu tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin da kuma zababben shugaban Ukraine Petro Poroschenko. Idan dai za a iya tunawa dai, kasashe G7 sun yi kira ga shugaban Rasha da ya ba wa takwaran akinsa hadin kai idan ba ya so a ci gaba da mayar da shi saniyar ware, tare da kakaba wa kasarsa karin takunkumin karya tattalin arziki.

A gobe asbar ne sabon shugaban na Ukraine Petro Poroschenko zai fara aiki. Tuni dai manyan kasashen duniya suka nemi Putin da ya amince da zaben shugaban kasa da ya bai wa Ukraine damar komawa kan tafarkin demokaradiyya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal