1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar MDD da hukumomin Koriya ta Arewa

Usman Shehu Usman
December 9, 2017

A karon farko jami'an MDD sun gana da hukumomin Pyongyang bayan shekaru masu yawa inda suka tattauna kan makaman nukiliyan kasar

https://p.dw.com/p/2p44k
Nordkorea Kim Jong Un in Pjöngjang
Hoto: Reuters/KCNA

A karon farko jami'an MDD sun gana da hukumomin Koriya ta Arewa bayan shekaru masu yawa. Jeffrey Feltman babban jami'in MDD ya kammala ziyarar kwananki biyar a Pyongyang, inda a yanzu ya isa Beijin babban birnin kasar China. A ganawar ta su Koriya ta Arewa ta zargi Amirka da haddasa zaman dar-dar a yankin. Amma duk da haka dai hukumomin Pyongyang sun yi alkawari ci gaba da tuntuba tsakanins da MDD. Ziyarar ta zo ne mako guda bayan da Koriya ta Arewa ta harba wani makamin linzami, wanda kan iya kai wa ga ko'ina na cikin kasar Amirka. A yayin ziyarar dai Jeffrey Feltman, ya gana da ministan harkokin waje Ri Yong-Ho da kuma karamin ministan harkokin waje Pak Myong-Kuk. Wannan shi ne karon farko da wani jami'in MDD ya ziyarci Koriya ta Arewa tun shekara ta 2010