Ganawar Jong-Un da Trump na neman rugujewa
May 16, 2018Koriya ta Arewa ta yi barazanar soke ganawar da aka shirya za a yi a watan gobe tsakanin Shugaba Kim Jong Un da kuma Shugaba Donald trump na Amirka da nufin kawo karshen zaman doya da man ja da kasashen suka share shekaru suna yi.
Kamfanin dillancin labaran kasar ta Koriya ta Arewa na KCNA ya ruwaito a wannan Laraba mataimakin ministan harakokin wajen Koriyar Kim Kye Gwan na cewa idan dai har mahukuntan kasar ta Amirka suka nemi tilasta wa Koriya ta Arewar neman ta yi watsi da shirinta na nukiliya ba ta hanyar fahimtar juna ba, to kuwa babu amfanin hawa tebirin tattaunawar da Amirkar.
Mataimakin ministan ya kuma ce za su ma sake nazari kan ko ya dace su amince da ganawar da aka shirya shugabannin kasashen biyu za su yi a nan gaba. Kasar Amirka dai na son ganin Koriya ta Arewa ta yi watsi kwata-kwata da shirinta na nukiliya kamar yadda kasar Libiya ta yi a lokacin mulkin Shugaba Mu'ammar Gaddafi, batun da ministan harakokin wajen Koriya ta Arewar ya ce ba za ta taba yiwuwa ba.
Kazalika Koriya ta Arewar ta sanar da soke wata ganawa mai muhimmanci da aka shirya za a yi tsakanin shugabannin Koriyoyi biyu wannan kuwa domin nuna rashin amincewarsu da atisayen sojoji na shekara-shekara da Koriya ta kudu ke gudanarwa a yanzu haka da kasar Amirka a yankin.