Ganawar farko a tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu
April 27, 2018Talla
Wannan shi ne karon farko a shekaru goma da shugabanin za su hadu da juna, a cikin wani yanayi na anashuwa, shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya fadawa takwaransa Kim Jung Un, ya yi matukar farin ciki da wannan ganawa ya kuma ce a yau an kama hanyar kafa tarihi.
Tuni dai shugabanin sauran kasashen duniya suka soma baiyana fatansu na ganin an bude sabon babi na tarihi a wannan ganawar don warware rikicin da ke a tsakaninsu bisa shirin nukiliyar kasar Koriya ta Arewa. An yi zaman ne a kauyen Panmunjom da ke yankin Koriya ta Arewa. Wannan na zuwa ne bayan da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jung Un a makon da ya gabata ya yi alkwarin jingine shirin nukiliyar kasar.