1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa tsakanin jami'an Amirka da Koriya ta Arewa

Zulaiha Abubakar
April 18, 2018

Shugaban hukumar leken asirin kasar Amirka Mike Pompeo  ya ziyarci kasar Koriya ta arewa don wata ganawar sirri da shugaban kasar Kim Jong Un.

https://p.dw.com/p/2wEJA
USA Mike Pompeo
Hoto: Getty Images/AFP/S. Loeb

Ganawar Sirrin na zuwa ne a daidai gabar da kasashen biyu masu gaba da juna ke shirin wani taro irin sa na farko bayan tsamin dangantakar da ya samo asali tun yakin kasashen Koriya.

A baya dai Donald Trump ya bayyana cewar Amirka da Koriya ta Arewa na tattauna wasu batutuwa masu tsauri kai tsaye, kodayake kakakin fadar mulki ta White house Sarah Sanders ta shaidawa manema labarai cewar babu wata tattaunawar kai tsaye da ta gudana tsakanin shuwagabannin biyu.

A halin yanzu Trump na shirye-shiryen ganawar da zasu yi a watan Yulin wannan shekara don ganin an kawo karshen shirin makami mai linzami na kasar ta Koriya ta arewa wanda ke barazana ga Kasar Amirka.