Gabashin birnin Kudus babban birnin Falasdinu
December 13, 2017Talla
Recep Tayyip Erdogan ya yi wannan kira ne a wajen taron kungiyar kasashe Msulmi OIC ko kuma OCI da ke gudana a birnin Istanbul. Sai dai a halin da ke ciki kasashe da dama na Musulmi ba sa son yin ja in ja da Amirka da kuma ma Isra'ila. Amma dai tuni da kasashen Iran da Jodan da Qatar da Libanon da kuma Sudan wadanda shugabanninsu ke halarta taron suka amsa kira na shugaban Turkiyya.