Tattalin arziki
G20: Taro kan bunkasa abinci a duniya
January 22, 2017Talla
Taron da ke gudana a birnin Berlin fadar gwamnatin Tarayyar Jamus zai hada da kwararru a bangaren noma daga kasashen kungiyar ta G20 masu bunkasar tattalin arziki. Kazalika mahalarta taron zasu jaddada bukatar alkinta ruwa da inganta harkokin noma na zamani. Taron da ke bangaren bukin "makon kare muhalli" a nan Jamus da ake kira da "Grünner Woche" na zama irinsa na farko da kungiyar kasashe masu bunkasar tattalin arzikin na G20 ke gudanarwa a wannan shekara. A wannan Asabar din dai, kimanin mutane dubu 10 ne suka gudanar da gangami a birnin na Berlin, a wani mataki na neman a inganta sashen noma.