1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G20:Merkel za ta gana da shugabannin Afirka

Salissou Boukari
June 12, 2017

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da ke a matsyin shugabar kungiyar G20 za ta gana da wasu shugabannin Afirka domin janyo hankalin masu zuba jari ya zuwa kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/2eVBL
Argentinien - Bundeskanzlerin Angela Merkel besucht Präsident Mauricio Macri
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da kasarta ke jagorancin kungiyar G20.Hoto: Reuters/M. Brindicci

Daya daga cikin masu magana da yawun shugabar gwamnatin ta Jamus, ya ce burin dai shi ne na karfafa hulda ta yadda za a samu bunkasar tattalin arziki mai dorewa a kasashen na Afirka. A watan Maris ma dai da ya gabata lokacin zaman taron ministocin kudi na kungiyar ta G20, an gayyaci wasu ministocin kudin na Afirka da suka hada da na Cote d'Ivoire da Maroko da Rwanda da kuma Tunusiya, domin kulla wata hulda da aka yi wa lakabi da "Compact with Africa".

A wannan karo, kuma kasa da wata daya da babban zaman taron kungiyar ta G20 da zai gudana a birnin Hambourg na nan Jamus, Shugabar ta G20 Merkel, ta gayyoto shugabannin kasashen Ghana, Habasha, Jamhuriyar Nijar, Masar da Mali, inda za su zauna tare da manyan hukumomin kudi na kasa da kasa, wanda a cewar Shugabar Asusun bada lamuni ta Duniya Christine Lagarde, za su samar da hanyoyi ta yadda kasashen Kudu da Sahara za su samu bunkasa.