1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Francois Bozize ya arce zuwa Kamaru

March 26, 2013

Gwamnatin Kamaru ta tabbatar da cewar tsohon shugaban na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya shigo ƙasarta.

https://p.dw.com/p/184ed
The Central African Republic's President Francois Bozize looks on as he gives a press conference, on January 8, 2013 at the presidential palace in Bangui. Bozize refused on January 8 to discuss resigning at upcoming peace talks with rebels who have stormed across the country and seized several key towns. AFP PHOTO/ SIA KAMBOU (Photo credit should read SIA KAMBOU/AFP/Getty Images)
Francois BozizeHoto: AFP/Getty Images

Tun can da farko an riƙa baza labarin cewar tsohon shugaban ya arce zuwa Jamhuriyar Kwango tare da iyalensa, bayan da yan tawayen suka ƙwaci iko da birnin Bangui da kuma fadar shugaban ƙasar. To amma lokacin kaɗan sai aka samu labarin cewar gwamnatin Kamaru ta ba da sanarwar ta hayar kafofin yaɗa labarai cewar Francois Bozize yana a Yawunde.

Sanarwar da gwamnatin Kamaru ta bayyana a kan kafofin yaɗa labarai

Wata yar jaridar ta gidan talbijan da rediyio na ƙasar ta Kamaru wato CRTV ta bayyana sanarwar ta na mai cewar gwamnatin Kamaru ta na kira da a dawo da kwanciyar hankali a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, bayan wani juyin mulkin da sojojin suka yi wanda ya kifar da gwamnatin Francois Bozize. A ƙarshe kuma ta ce sanarwa gwamnatin na cewar shugaban ya samu mafuka a Kamarun. Hukumomin na Kamaru sun samarwa da tsohon shugaban masabki a cikin wani babban Hotel ɗin da ke a birin Yawunde.

paul biya_right.jpg French President Jacques Chirac, center, listens to President of Burkina Faso, Blaise Campaore, left, with the President of Gabon, Omar Bongo, front and President of Cameroon Paul Biya, right, during the French-Africa Summit in Cannes, southern France, Friday, Feb. 16, 2007.(AP Photo/Lionel Cironneau)
Paul Biya shugaban ƙasar KamaruHoto: AP Photo

Wata motar soji ce ta ɗauki tsohon shugaban ƙasar Francois Bozize zuwa Hotel Hilton da ke a birnin Yawunde, Inda aka yi masa masabki. Kuma jama'a sun yi dandazo a bakin Hotel ɗin suna kallon yadda sojojin suka zagaye ginin na Hotel ɗin, kowane na furta albarkacin bakinsa. Cyprain Awudu Mbaya wani dan Majalisar Dokoki ne. Ya ce : '' Na yi ido huɗu da Bozize ya ce na ga lokacin da sojojin da ke tsaron shugaban ƙasa suka kawo wani mutumin a Hotel ɗin wanda muka gano cewar hamɓarraren shugaban Afirka ta ta Tsakiyar ne.''

Jama'ar ƙasar na bayyana fargaban su akan zuwan tsohon shugaban

Ƙasar ta Kamaru na raba iyaka mai girma da Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya, kuma daman kusan zaman doya da man ja ake yi tsakanin ƙasashen biyu, a farkon shekarar bana yan tawayen na ƙungiyar Seleka sun tsallaka suka shiga Kamarun inda suka kashe sojoji guda uku a garin Kenzu. Ɗan majalisar dokoki Cyprain Awudu ya ce suna da fargaba. Ya ce :'' Ya kamata gwamnati ta ɗauki matakai masu tsauri domin kare iyokokin mu, ya ce wannan nauyi ne da ya rattaya akan wuya gwamnati.''

Central African Republic President Francois Bozize (centre L, in blue) speaks to a crowd of supporters and anti-rebel protesters during an appeal for help, in Bangui December 27, 2012. Bozize on Thursday appealed for France and the United States to help push back rebels threatening his government and the capital, but Paris said its troops were only ready to protect French nationals. The exchanges came as regional African leaders tried to broker a ceasefire deal and as rebels said they had temporarily halted their advance on Bangui, the capital, to allow talks to take place. Picture taken December 27, 2012. REUTERS/Stringer (CENTRAL AFRICAN REPUBLIC - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Francois Bozize a tsakiyar sojojiHoto: Reuters

Wannan dai ba shi ba ne ,karo na farko da wani hamɓarraren shugaba na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da yake neman mafukar siyasa a Kamaru, tsohon shugaban ƙasar ma, da aka yi wa juyin mulki a shekarun baya wato Ange Felix Patase ,shi ma ya nemi mafuka a Kamaru a wani lokacin.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal