1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Indiya na ziyara a Turai

Yusuf Bala Nayaya
May 30, 2017

Kasar Indiya na son karfafa hulda tsakaninta da Jamus, a wani mataki na kokarin habaka tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/2dnqW
Deutschland Meseberg - Angela Merkel trifft auf Premierminister Modi
Hoto: Reuters/F. Bensch

Tuni dai Firaministan kasar Indiya Narendra Modi ya gana da shugabar gwamnatin Jamus din Angela Merkel tare da ministocinta a Berlin babban birnin kasar, a dai-dai lokacin da Indiyan da ke zama babba daga yankin Asiya ke son kara inganta dangantakar tattalin arziki da Jamus da ke zaman kasar da ke kan gaba ta wannan fuska a tsakanin kasashen Turai. Firaminista Modi da Merkel za su zauna su sake bude babi a tattaunawar huldar kasuwanci da zuba jari mara shinge tsakanin EU da Indiya, abin da ke zuwa bayan da mahukuntan Beijing ke kara azama a fannin hulda da kasashen na Turai, inda tuni Firaministankasar ta China Li Keqiang ke shirin kawo wata ziyara zuwa birnin na Berlin cikin wannan mako.

A yayin ganawar tata da Firaministan na Indiya dai, Merkel ta sake jaddada cewa dole ne Jamus da kungiyar Tarayyar Turai ta EU su tashi tsaye, domin kulla hulda da kasashen da arzikinsu ke bunkasa. A ranar Lahadin da ta gabata ne dai Merkel din ta bayyana cewa Jamus ba za ta sake sakin jikin tare da ci gaba da bin tsarin al'adawajen takaita huldarta da kasashen Amirka da Birtaniya ba, musamman a wannan lokaci na gwamnatin Shugaba Trump da kuma yadda Birtaniya ta zabi ta fice daga kungiyar EU.