Ethiopia: Abiy Ahmed ya samu lambar yabo ta Nobel
October 11, 2019Kwamitin da ke bayar da kyautar ta Nobel, ya mika kyautar bana ga shugaban ne a bisa kokarin samar da zaman lafiya a kasar ta Habasha da ta sha fama da rikici da kuma sauye-sauyen da ya kawo tun bayan da ya karbi ragamar mulki a watan Afrilun 2018.
A yayin da ya ke kokarin daidaita kasarsa da ke fuskantar tarin matsaloli, Firaiminsta Aby ya dauki matakin shiga tsakani a rikicin kasar Sudan da yayi awon gaba da gwamnatin Oumar al-Bashir, yunkuri ne na ganin an kawo karshen zub da jini tare da hawa kan teburin sulhu don samar da zaman lafiya, mataki ne dai da ya yi tasiri, daya daga cikin nasarorin da ya kai ga lashe wannan kyautar.
Rikicin kabilanci da ya dabaibaye kasar Habasha kafin ya soma mulki ya raba miliyoyi da gidajensu, baya ga haka akwai batun samar da zaman lafiya a tsakanin kasar da makwabciyarta Eritriya, wasu daga cikin kalubalen da ke gaban shugaban kenan da ake ganin lashe kyautar ka iya kara masa kwarin gwiwa wajen ganin ya ceto kasar daga durkushewa.