Filayen kwallon kafa mafiya shahara a Turai
Manyan kungiyoyin kwallon kafa da suka fi suna a wasannin lig-lig a Turai na amfani da kasaitattun wuraren taka leda a biranen Munich da Madrid da London da Milan, lamarin da ya sa suka yi ficce a duniya.
Filin wasa na Puskás Aréna, Budapest, Hungari
Puskás Aréna na Budapest yana cikin sabbin filayen kwallon kafa na Turai tun 2019 da aka bude. An saka wa filin sunan Ferenc Puskás shahararren dan wasan kasar Hungari, kuma ginin shi ne mafi girma na gwamnati a kasar. A 2021 filin ya karbi gasar cin kofin nahiyar Turai ta UEFA da kuma wasan karshe na cin kofin Europa Lig a shekarar 2023. Filin na daukan 'yan kallo kimanin 67,215.
Filin Signal Iduna Park, Dortmund, Jamus
A gidan kungiyar Borussia Dortmund tun 1974 akwai abubuwa masu kayatarwa da tarihi da nasarorin da kungiyar ta samu. Filin wasan yana da bango mai ruwan dorawa kuma yana da wurin da 'yan kallo ke tsayuwa mai ban sha'awa. 'Yan kallo suna son gidan tarihin kungiyar mai launin baki-da-ruwan dorawa domin girmama kungiyar.
Allianz Arena, Munich, Jamus
Allianz Arena gidan kungiyar Bayern Munich, ya yi suna saboda sauya launi ta amfani da hasken fitilu 2,800. Ana zagayawa da masu yawon bude ido a wureren da 'yan wasan ke sauya kaya, da hanyar fitowa zuwa filin kwallon, gami da gidan ajiye kayan tarihi. Filin na daukan 'yan kallo 75,000 kuma shi ne na biyu mafi girma a Jamus.
Filin Santiago Bernabéu, Madrid, Spain
Santiago Bernabéu, an kammala ginisa a 1947, kungiyar Real Madrid na amfani da shi fiye da shekaru 70. Yanzu haka ana gyaransa, an takaita masu masu kai ziyara. Duk da haka ana ziyara gidan tarihin. Filin wasan yana duakar 'yan kallo 81,000 da kayayyaki na zamani kuma ya kasance mai tasiri a birnin.
Filin Camp Nou, Barcelona, Spain
Babu abin da yake wakiltar birnin Barcelona fiye da filin wasa na Camp Nou na kungiyar FC Barcelona. An gina shi a shekarar 1957, yana daukar mutane 100,000 mafi girma a Turai. Saboda gyara da ake yi, kungiyar Barcelona ta yi kakar wasannin 2023/24 a Filin wasa na Olympic.
Filin Wembley, London, Birtaniya
Wembley — sunan wannan filin wasa na London ya shahara a shekaru 100 da suka gabata, kuma a wannan fili kadai Ingila ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, kuma a shekarar 2003, an yi gyara a filin da yi masa kwalliya. Ana kuma wake-wake a filin.
Filin Old Trafford, Manchester, Ingila
Old Trafford ana kuma kiransa da 'Theatre of dreams,' kamar yadda tsohon shahararren dan wasan kungiyar Manchester United, Bobby Charlton ke kira. Lokacin Yakin Duniya na Biyu sojojin sun yi amfani da filin, kuma jiragen saman yaki na Jamus sun lalata shi ta hanyar ruwan bama-bamai a shekarar 1941. Filin na Manchester United yana daukar 'yan kallo 75,000.
Filin Anfield, Liverpool, Ingila
Kwanan nan aka gyara filin Anfield, gidan kungiyar Liverpool wanda yake daukar 'yan kallo 54,000. Duk bangarorin filin wasan suna dauke da tarihi na 'yan wasan da suka taka rawar gani.
Filin Giuseppe Meazza, Milan, Italiya
Duk da a hukumance sunan filin wasan Giuseppe Meazza, amma ana kiransa da tsohon sunan, San Siro. Yana daukar mutane 75,000. Ya kasance gida ga kungiyoyi biyu na birnin: AC Milan da Inter Milan. Filin wasan ya kwashe kimanin shekaru 100, kuma shirin rushe wani bangare na filin ya janyo cece-kuce.
Filin Stade de France, Paris, Faransa
Shi ne filin wasa mafi girma a Faransa da aka gina a shekarar 1998 lokacin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, yana da rumfa na musamman da ke rufe duk yawan wuraren zama 80,000. Ana wasannin kwallon kafa da zari-ruga da sauran wasanni a ciki. A shirin wasannin guje-guje na duniya a shekara ta 2024 da birnin Paris zai dauki nauyi, za'a ingata tashar jirgin kasa da ke kai wa zuwa filin wasan.