FIFA ta haramta wa Samuel Eto'o shi wasanni
September 30, 2024Samuel Eto'o wanda shi ne shugaban hukumar kwallon kafan Kamaru tun shekara ta 2021, an yanke masa hukuncin haramcin shiga wasannin bisa wasu laifuka biyu da ake tuhumar ya aikata a gasar cin kofin kwallon kafan mata 'yan kasa da shekaru 20 na bana a kasar Kolombiya. FIFA bata kai ga yin karin haske kan laifukan da Samuel Eto'o ya aikata ba a gasar da Burazil ta lashe da doke Kamarun ci 3-1, wanda dakyar Burazil ta samu galaba kan kasar Kamarun bayan garin lokacin wasa. Hukumar ta kwallon kafa ta ce haramcin na watanni shida ne, kuma tsawon wadannan watanni an haramta wa Eto'o shiga filin wasa na dukkan nau'in wasanni walau na mata ko na maza, wasan na matasa ne ko na manyan yan wasa, duk haramcin ya hau a kansa. Mai shekaru 43 Eto'o, ya halarci dukkan wasannin cin kofin kwallon kafan duniya da Kamarun ta halarta daga shekara ta 1989 izuwa 2014 in banda shekara ta 2006. Bayan cin lambobin yabo ya wasannin gida, ya kuma ci nasarorin da yawa kama da kulob din Barcerlona da kuma Inter Milan.