1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

FIFA ta fitar da sunayen Messi da Mbappe da Haaland a 2023

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 14, 2023

Za a sanar da wanda ya yi nasara a bikin da za a gudanar a birnin London na Burtaniya ranar 15 ga watan Janairun 2024

https://p.dw.com/p/4aAcv
Hoto: Harold Cunningham/Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar da jerin sunayen 'yan wasa uku da za a zabi gwarzon shekara a ciki, a wannan shekara mai kare wa ta 2023.

'Yan wasan sun hada da Lionel Messi na kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami da ke Amurka, wanda ya jagoranci kasarsa ta Argentina wajen lashe gasar cin kofin duniya ta bara a kasar Qatar.

Karin bayani:FIFA: Kasashe uku za su dauki nauyin gasar 2030

Sai Kylian Mbappe 'dan kasar Faransa kuma 'dan kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain, sai na ukun su Erling Braut Haaland na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da ke Ingila kuma 'dan asalin kasar Norway.

Karin bayani:Gasar neman cin kofin duniya ta mata

Za dai a sanar da wanda ya yi nasara a bikin da za a gudanar a birnin London na Burtaniya ranar 15 ga watan Janairun sabuwar shekara mai zuwa.