FIFA za ta bayyana wadanda za su kara a Katar
March 31, 2022Talla
Taron wanda shi ne karo na 72, na cike da rarrabuwar kawuna a game da sabbin dokoki da hukumar ke son aiwatarwa, wadanda suka hada da dawo da gasar cin kofin duniyar na kwallon kafa a tsawon shekaru biyu a maimakon hudu, da kuma wasu sauye-sauyen a fanin gasar wasannin klub-klub. A gobe juma'a aka shirya hukumar za ta bayyana rukunin-rukuni na kasashen da zan su kara a zagaye na farko na gasar ta Katar bayan an yi wala-wala.