1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya na fatan sasantawa da abokan gaba

Lateefa Mustapha Ja'afar RGB
February 13, 2023

Shugaba Bashar al-Assad na Siriya na kokarin ganin kasarsa ta fita daga matsayin saniyar ware a tsakanin al'ummomin kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/4NQUf
Shugaba Bashar al-Assad
Shugaba Bashar al-AssadHoto: Joseph Eid/AFP/Getty Images

A wani mataki na ba-zata, Shugaba Bashar al-Assad ya ce, zai yadda da bukatun al'ummomin kasa da kasa na amincewa a kai kayan agaji zuwa ga yankunan da ke karkashin 'yan tawaye da girgizar kasar ta shafa. A baya, tilas sai kayan agajin sun bi ta Damaskus babban birnin kasar, wanda ke karkashin iko gwamnatin Assad din.

Wannan mataki na Shugaba Bashar al-Assad na zuwa ne, a daidai lokacin da yake fatan ganin an dage takunkuman da aka kakabawa kasarsa Siriya. Sai dai har kawo yanzu babu tabbacin cewa, kungiyar Tarayyar Turai EU za ta yi maraba da wannan mataki na Assad da ke nuni da cewa tilas sai ta yi hulda da gwamnatinsa. A farkon wannan makon, kamfanin dillancin labaran Damaskus SANA, majalisar dokokin Siriyan ta yi kira ga al'ummomin kasa da kasa da su gaggauta cire takunkuman da suka kakaba mata da ta bayyana da na rashin adalci da ke matukar shafar rayuwar al'ummar kasar.

An fuskanci tsaiko a isar da agaji Siriya
An fuskanci tsaiko a isar da agaji SiriyaHoto: Ahmed Saad/REUTERS

A nasa bangaren jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Siriya, ya bukaci al'ummomin kasa da kasa su kawo dauki, a daidai lokacin da ministan harkokin kaashen ketare na Siriya ke cewa, takunkumin da Amirka da kungiyar Tarayyar Turai EU suka kakabawa kasarsa na dakile daukin da ake son kai wa ga wadanda girgizar kasar ta shafa.

Al'ummar arewacin Siriya dai, sun tsinci kansu cikin wannan ibtila'i ne a daidai lokacin da suke cikin tsaka mai wuya na tsawon shekaru da kasarsu ta kwashe tana fama da yaki. Birnin Jandaris da ke yankin Arewa maso Yammacin Siriya na zaman guda, daga yankunan kasar da ke karkashin ikon 'yan tawaye kuma ya kasance yankin da girgizar kasar ta yi wa mummunar illa. Yadda hanyoyi suka laalace, na zaman babban kalubale ga jami'an agaji. Jami'an agajin dai, na yin kira da a bude hanyoyin kai agaji musamman ga yankin arewacin Siriyan da yakin sama da shekaru 10 ya dai-dai-ta. Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana bukatar kai daukin gaggawa ga kasar da ya ce, ba a manta da bala'in girgizar kasar da ya same ta ba.

Mutum sama da 10,000 sun mutu a girgizar kasar
Mutum sama da 10,000 sun mutu a girgizar kasarHoto: Hussein Malla/AP/picture alliance

Girgizar kasar dai, ta kara ta'azzar yanayin bukatar tallafin jin kan da ake fama da shi a kasar da ta kwashe tsawon shekaru 12 cikin yakin basasa. Tuni kasashen Yamma suka fara tura tallafi zuwa ga gwamnatin Damaskus da suke gaba da ita, sai dai kuma Turkiyya ta bude kan iyakarta da Siriya da ke garin Bab al-Hawa. Hakan dai ya bai wa motocin dakon kaya makare da kayan agaji daga Majalisar Dinkin Duniya damar kai dauki, har ma ga yankunan da 'yan tawaye da Kurdawa ke rike da su. 

A hannu guda kuma tuni kasashen Larabawa da a baya suka yanke hulda da Siriyan suka fara mika taimakonsu, inda rahotanni ke nuni da cewa hatta shugaban Masar Abdel-Fattah el-Sissi ya kira Shugaba Assad ta wayar tarho a karon farko tun bayan barkewar yaki a Siriya. Haka ma kasashen Katar da Oman, sun aike da tallafinsu ta hanyar Turkiyya domin kai wa al'ummar Siriya yayin da Iraki ta jaddada bukatar dawo da Siriyan cikin kungiyar Kasashen Larabawa.