1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farinjinin shugabar Brazil na karuwa

September 27, 2014

Yayin da kasa da mako biyu ya rage a yi zaben kasar Brazil, shugabar kasar da ke neman wa'adi na biyu, na kara samun tagomashi wajen al'ummar wannan kasa.

https://p.dw.com/p/1DLy2
Hoto: picture-alliance/dpa/Antonio Lacerda

Shugabar kasar Brasil Dilma Rousseff, da ke neman wa'adi na biyu a zaben shugaban kasar da zai gudana a watan Octoba, na ci gaba da samun karbuwa daga masu kada kuri'a a wannan kasa, inda a halin yanzu take kan gaba da tazara a gaban babbar abokiyar hammayarta Marina Silva.

A wani binciken jin ra'ayin jama'a na baya-bayannan, Rousseff na kan gaba da kashi 40 cikin 100, yayin da abokiyar hamayyarta Silva ke da kashi 27 cikin 100, inda hasashen ya nunar cewa, idan ma har aka dawo zagaye na biyu, Shugaba Rousseff din na iya cin zaben da kashi 47 cikin 100 a gaban abokiyar hamayyarta wadda ake hasashen za ta samu kashi 43 cikin 100 a zagayan na biyu.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba