Farfado da zirga-zirgar jiragen kasa a kasashen Koriya
June 26, 2018Talla
A wata tattaunawa da shugabannin gwamnatocin Koriyoyin biyu suka yi a wannan Talata a kauyen Panmunjom na kan iyakar kasashen biyu, sun bayyana bukatar gyara tsohuwar hanyar jirgin kasa ta tsakanin biranen Seoul da Pyongyang zuwa Sinuiju na kan iyaka da kasar Chaina, hanyar da kasar Japan ta gina tun a farko karni na 20 kafin soma yakin da ya kai ga raba hadaddiyar kasar Koriyar gida biyu.
Wannan dai shi ne karo na farko a shekaru 10 da Koriyoyin biyu suka tattauna kan wannan batu na farfado da zirga-zirgar jiragen kasa a tsakaninsu. Farfado da wannan zirga-zirga ta jiragen kasar zai bai wa Koriya ta Kudu damar fitar da hajojinta ta kasa zuwa kasashen Chaina da Rasha da ma na Turai.