Halin kuncin da fararen hula ke ciki a Yemen
July 31, 2015Kungiyar da ta yi korafin a baya-bayan nan dai ita ce ta Likitoci na Gari na Kowa wato "Doctors Without Borders" da Turancin Ingilishi. Shugabar kungiyar Joanne Liu ce ta yi korafin a wata hira da ta yi da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP a Sanaa babban birnin kasar ta Yemen da ke karkashin jagorancin 'yan tawayen Houthi. Liu ta ce hana shigar da kayan agaji Yemen din da Saudiya ta yi na kashe dinbin fararen hula kamar yadda yakin da take jagoranta ke kashe fararen hular a hannu guda. Ta kara da cewa yanayin da fararen hular ke ciki abin takaici ne ganin cewa dama can mafi yawan al'ummar Yemen sun dogara ne ga tallafin da suke samu daga kungiyoyin agaji. Wannan sabon rahoto na halin da fararen hular na Yemen ke ciki na zuwa ne a dai-dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce har yanzu Saudiyan ba ta bayar da ko sisi ba daga cikin kudin da ta yi alkawarin bayarwa domin agazawa Yemen din wanda yawansu ya kai dalar Amirka miliyan 274.