1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransawa ba sa son yaki a Mali

Abdoulaye Mamane Amadou
January 12, 2021

A karon farko wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da a ka gudanar a Faransa, ta nuna cewa akasarin 'yan kasar ba sa goyon bayan ci gaba da yaki da 'yan ta'adda da kasar ke yi a Mali.

https://p.dw.com/p/3noAx
Symbolbild- Nigera - Militärübung
Hoto: picture-alliance/dpa/P. de Poulpiquet

Binciken cibiyar IFOP da aka wallafa a mujallar Le Point ya nuna cewa kaso 51,% na al'ummar Faransa basa son ci gaba da yaki da 'yan ta'adda a Mali, adadin da ya kasance mafi rinjaye idan aka kwatanta da wadanda suka nuna amincewarsu lokacin da Faransa ta shiga yaki da 'yan ta'adda a Mali a shekarar 2013.

Wannan lamarin na zuwa ne bayan wasu hare-haren ta'addanci biyu da suka hallaka sojojin Faransa biyar a farkon watan Janairun 2021 a Mali.