Faransa: Zanga zangar adawa da harajin mai
November 17, 2018A kasar Faransa direbobin motocin haya sun yi wa manyan hanyoyin kasar shinge a ci gaba da zanga-zangar adawa da karin kudin harajin mai da gwamnatin kasar tayi.
Rahotanni sun ce mace daya ta rasa ranta yayin da wasu mutanen 47 kuma suka sami raunuka yayin arangama da jami'an tsaro.
Masu zanga-zangar dai sun yi dafifi a dukkanin shatale-tale da kuma manyan titunan da suka zagaye birnin Faris a wannan asabar din, wannan karin haraji a kudin man ababen hawa guda ne daga cikin kudirorin shugaban kasar Emmanuel Macron na rage amfani da man dake gurbata yanayi duk kuwa da cewa wannan mataki na zaman barazana ga dorewar farin jinin shugaban tsakanin al'ummar kasar.
A ranar Juma'a ne kuma motocin daukar marassa lafiya na kasar suka gudanar da tasu zanga-zangar don matsawa gwamnati ta biya musu wasu bukatunsu .