Faransa ta sanar rufe masallaci mafi girma a birnin Paris
October 20, 2020A cigaba da binciken da hukumar 'yan sandan Faransa ke yi, bayan kisan da aka yi wa wani malamin makaranta a kasar wanda ya nuna hotunan batancin da aka yi wa manzon Allah ga dalibansa, ma'aikatar cikin gidan Faransa ta bayar da sanarwar rufe masallaci mafi girma a kasar daga gobe Laraba.
Rufe masallacin da ke gabacin birnin na Paris, ya biyo bayan wani faifan bidiyon jan kunnen malamin makarantar da aka wallafa a shafin masallacin na facebook kwanaki kalilan gabanin kisan da aka yi masa.
Masallacin mai yawan masallata dubu daya da dari biyar, zai kasance a garkame har na tsawon watanni shida ya yin da ake cigaba da bincike a cewar ministan harkokin cikin gida Gerald Darmanin.
Tuni dai rundunar 'yan sandan Faransa ta kaddamar da bincike tare da kamen mutane masu alaka da wasu kungiyoyin kishin islama.