Faransa za ta rage sojinta a yakin Sahel
January 8, 2021Talla
Shugaba Macron ya bayyana hakan ne a yayin da yake ta'aziyyar mutuwar wasu dakarun sojin kasar a wani hari da aka kai musu a kasar Mali. An gudanar da taro a birnin Paris domin tunawa da sojojin biyu da suka rasa rayukansu a fagen yaki da 'yan ta'adda. Ana sa ran zai yi cikkaken bayani a wani taron koli da ya kunshi babban shirin rundunar sojin Faransa a birnin Ndjamena na kasar Chadi a watan gobe.
Ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drian ya ce akalla dakarunsu dubu biyar ne za su janye daga yanklin na Sahel. Tun a shekarar 2013 ne sojin Faransa suke a kasar Mali kafin daga bisani a wani mataki na tabbatar da karin tsaro a yankin suka bazu har ya zuwa kasashen Chadi da Nijar da Burkina Faso da kuma Moritaniya.