Nijar: Zargin Faransa da kutse a siyasa
February 11, 2021Zargin nasu dai ya yi karfi ne bayan da jakadan Faransa a Jamhuriyar ta Nijar, ya kai ziyara gidajen 'yan takarar shugabancin kasar biyu da za su fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, ranar 21 ga wannan wata na Fabarairu da muke ciki. Tun dai gabanin zagaye na farko na zabukan da aka yi a Nijar din, wasu 'yan kasar suka soma zargin Faransa da yin katsalandan a harkokin zaben na Nijar, musamman ganin dan takarar jam'iyya mai mulki ya kai ziyara Faransa.
Karin Bayani: Kaddamar da yakin neman zabe a Nijar
Sai dai lamari na baya-bayan nan da ya kara haddasa muhawarar da ma bayyana 'yan takarar biyu a matsayin 'yan amshin shatar Faransa, shi ne ziyarar da sabon jakadan Faransan a Nijar ya kai gidajen 'yan takarar guda biyu makwanni biyu gabanin zagaye na biyu na zaben shugaban kasar. Hashimou Abdourahmane shugaban kungiyar daliban jami'ar birnin Yamai, na daga cikin masu irin wannan zargi.
To sai dai a lokacin da wasu 'yan Nijar ke zargin Faransa da yin katsalandan a harkokin zaben Nijar, wasu na ganin Faransar na kokari ne na share fagen ci gaba da kare muradunta a Nijar din a wajen kowane daga cikin 'yan takarar da zai zamo shugaban kasa. Malam Nouhou Arzika shahararren dan fafutukar nan kana shugaban kungiyar MPCR na daga cikin masu irin wannan tunani.
Karin Bayani:Wacce alkibla siyasar Nijar ta dosa?
Koma dai mai ake ciki, da dama cikin al'ummar Jamhuriyar ta Nijar, na ganin ko ma wanene zai zamo shugaban kasa daga cikin 'yan takarar guda biyu, to kuwa ba abin da zai sauya a game da dangantakar kut da kut da ke tsakanin Nijar din da Faransa, domin kuwa dangantaka ce irin ta mutu ka raba takalmin kaza, in ji Bahaushe.