Barazanar kara yaduwar corona a Faransa
July 14, 2020Talla
Kwararru a kan sha'anin kiwon lafiya sun yi kashedi kara yaduwar annobar corona a zagaye na biyu bayan kisan sama da mutane dubu 30 da cutar ta yi a cikin watannin biyu da suka gabata a Faransar. Wasu manyan likitoci sun bukaci gwamnatin da ta tilasta saka takunkumin rufe fuska ya zama dole ko'ina a cikin wuraran da jama'a ke taruwa.