1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

FAO: Matsalar yunwa ta karu a duniya

Ramatu Garba Baba
October 12, 2017

Hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya FAO ta sanar cewa matsalar yake-yake gami da sauyin yanayi da ake fuskanta sun mayar da hannun agogo baya a kokarin da ake na kawar da yunwa daga doron kasa.

https://p.dw.com/p/2ljbo
Hunger in Somalia
Rabon abinci ga masu matsalar yunwa a SomaliyaHoto: picture-alliance/Photoshot

Daga cikin kasashe 111 da aka gudanar da binciken, kiddidiga ya nuna cewar rabin wadannan kasashen na fuskantar tsananin rashin abinci mai gina jiki duk da cewa a baya an nunar da cewa yawan mutanen da ke fama da yunwa a duniya ya ragu, sai dai kumar ta ce rikice-rikicen yaki da kuma matsalar sauyin yanayi suka haifarwa da mayar da hannun agogo baya kan wannan nasara da aka yi ikarrarin samu a cewar hukumar wadda ta ce matsalar ta fi Kamari a Jihohin Arewa Maso Gabashin Najeriya da Somaliya da Yemen da ake fuskantar yakin basasa.

Hunger in Somalia
Jerin masu neman abinci a SomaliyaHoto: picture alliance/AP Photo/F. A. Warsameh

Kasar Yemen tana mataki na shida a cikin kasashen da al'ummarsu ke fuskantar tsananin yunwa tun bayan barkewar yaki a kasar a shekara ta 2015. Wakilin kasar ta Yemen a Majalisar Dinkin Duniya Ould Cheikh Ahmed, ya bayyana takaicinsa kan halin da kasar ke ciki:

"Halin da ake ciki babu wanda ya yi nasara a yakin kasar saboda haka ina kira ga bangarorin da ke rikici da juna da su rungumi zaman sulhu don warware rikicin ganin illar da yunwa ke yi wa al'umma.''

Ana ganin zai yi wuya a cimma muradun karni kan batun kawar da yunwa daga doron kasa kamar yadda aka yi hasashe a baya. Binciken hukumar kula da abincin ta Majalisar Dinkin Duniya ya ci gaba da cewa kiddidiga da aka yi a watan da ya gabata  alkaluman sun haura, inda matsalar yunwa ta shafi mutane miliyan dari takwas da goma sha biyar, kuma mata da yara kanana na daga cikin wadanda suka fi fuskantar matsalolin da yunwa ke haifarwa.