1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fahimtar juna tsakanin Trump da Kim

Mohammad Nasiru Awal
March 9, 2018

Shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-In ya bayyana shirin ganawar da ake yi tsakanin shugaban Amirka Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un zai zama muhimmmin mataki zaman lafiya

https://p.dw.com/p/2u3e0
Karikatur Nordkorea USA Atomwaffen

Shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae In ya bayyana shirin ganawar da ake yi tsakanin shugaban Amirka Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un zai zama muhimmmin mataki a kan hanyar samar da zaman lafiya a yankin tsibirin Koriya. Su ma manyan kasashen duniya ciki har da China da Rasha sun yi maraba da shirin ganawar tsakanin shugabannin biyu da suka dade suna sukar lamirin junm suna kuma yi wa juna barazana. Mohammad Nasiru Awal na dauke da karin bayani.

A lokacin da yake jawabi a wata liyafa gabanin bude wasannin Olympics na nakasassu a wannan Jumma'a, shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae In ya ce za a tuna da taron kolin da ake shirin gudanarwa tsakanin Amirka da Koriya ta Arewa a matsayin wani abin tarihi da zai ba da gudunmawa wajen samar da tsaro a yankin tsibirin Koriya, inda ya kara da cewa taron tsakanin shugaban Amirka Donald Trump da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un zai dora shirin kwance damarar makaman nukiliya a yankin gaba daya kan mataki na karshe.

Karikatur: Trump und Kim (USA Nordkorea Atomstreit)

Ya ce: "A yau Shugaba Trump ya yi alkawarin ganawa jagoran Koriya ta Arewa Kim Jong Un a cikin watan Mayu. Shirin kwance damarar makaman nukiliya da samar da zaman lafiya a yankin tsibirin Koriya ya fara tabbata. Na yi imani wasannin Olympics na Pyeongchang da kokarinmu na samun zaman lafiya za su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a duniya baki daya. Yabo zuwa ga al'ummomin duniya da ke fatan samun zaman lafiya."

Kasar Sin wato China da ke zama kawar Koriya ta Arewa ta yi maraba da shirin tattaunawar da cewa kyakkyawar alama ce da ya zama wajibi dukkan bangarorin su nuna kuduri na siyasa. Shi ma a martanin da ya mayar ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, da ke rangadin wasu kasashen Afirka ya ce mataki ne a kan hanyar da ta dace.

Ya ce: "Da farko mun yi imani wannan mataki ne a kan hanyar da ta dace. Wannan shi ne karon farko da muka ji wannan shirin, kuma taron zai gudana n e domin rage zaman zullumi a yankin tsibirin Koriya. Muna kuma maraba da yarjejeniyar Seoul da Pyongyang ta gudanar da taron koli a cikin watan Afrilu. Da ma wannna shi ne abin da China da Rasha da ma sauran kasashe ke yi ta kira da a yi."

Shi ma a nasa bangaren sakataren harkokin wajen Amirka, Rex Tillerson da ke ziyara a nahiyar Afirka ya ce sauyin matsayi da jagoran Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya dauka shi ya tunzara Shugaba Trump yarda ya gana da shi.

Ya ce: "Shugaba Trump tun ba yau ba ya nuna shirin tattaunawa da Kim Jong Un da zarar dama ta samu, kuma yanzu lokacin ya yi. A kullum kofofinmu a bude suke na tattaunawa. Sai dai shugaba Donald Trump ne ya yanke shawarar tattaunawa da shugaban Kim Jong Un. Yanzu ya rage da mun sanya lokaci da kuma wurin da za a yi wannan ganawa ta farko tsakanin mutanen biyu."

Ita ma a martanin da ta mayar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce wannan cigaban ya tabbatar da nasarar takunkuman da kasashen duniya suka jajirce ka iya yi, tana mai cewa ya ba da wani fata bayan duniya ta kasance cikin damuwa dangane da shirin nukiliyar Koriya ta Arewa.