1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutukar neman sauyi a Chadi

Salissou Boukari/ASFebruary 12, 2016

Kungiyoyi da dama sun a Chadi sun fara fafutuka wajen ganin shugaban kasar Idriss Deby da ya yi shekaru 25 kan gadon mulki ba samu nasara ba azaben da ke tafe nan da watanni biyu.

https://p.dw.com/p/1HuhC
Tschad Präsident Idriss Deby
Hoto: picture-alliance/dpa/C. P. Tesson

Tun bayan da Shugaba Deby ya sanar da muradinsa na sake neman wani sabon wa'adi na shugabancin kasar a ranar Litinin da ta gabata ake ci gaban da samun tashin jijiyoyin wuya a Ndjamena babban birnin kasar da ma sauran biranen kasar. A baya dai batun adawa da mulkin na Idriss deby abu ne da ake yin shi da sannu a hankali, amma yanzu lamari ya fara zafafa.

Kungiyoyin fararen hula da ma dailibai da dama ne ke kan gaba wajen wannan fafutuka. Wani dalibi da ke kasar ya ce "ya kyautu Shugaba Deby ya duba abubuwan da suke gudana a wasu kasashe makwabta don haka kawai ya tafiyarsa shi, wannan shi ne kawai abinda muke bukata a halin yanzu.''

Suma dai 'yan jaridar na kafofin sadarwa masu zaman kansu a kasar ta Chadi sun kafa wata kungiya ta neman sauyi. Mai magana da yawun kungiyar Moussaye Doumla ''muna tsammani hakanmu za ta cimma ruwa ta ganin mun kwace mulki daga hannun mutun daya da ya yi kaka gida. Wannan ita ce hanya da za ta bada dama ga dukkan kungiyoyin da ke neman ci gaban wannan kasa."

Tschad Präsident Idriss Déby Itno
Shugaba Idris Deby da ya shafe shekaru 25 kan mulki na son sake samun wani sabon wa'adinHoto: DW/B. Dariustone

Baya ga masu fafutuka a cikin gida, 'yan Chadi din da ke kasashen ketare ma dai da dama na son ganin Deby ya bar mulki kazalika wannan batun na neman chanji a kasar abu ne da ake gani karara a cikin shafukan intanet na sada zumunta da musayar ra'ayi inda a kullum ake ganin mutane na tofa albarkacin bakunansu ba tare da sun boye kansu ba to sai dai a share guda magoya bayan tazarce da Deby din ke son yi su ma na ta kokari wajen neman goyon bayan jama'a don cimma wannan buri.