1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gaza kafa gwamnatin a Spain tun bayan zabe

Abdourahamane Hassane
September 24, 2023

A Spain Shugaban jam'iyyar masu raayin 'yan mazan jiya ta Alberto Nuñez Feijoo wanda jam'iyyarsa ta zo ta daya a zaben 'yan majalisar dokoki a watan Yulin da ya gabata, ba tare da samun rinjaye ba ya gaza kafa gwamnti.

https://p.dw.com/p/4Wki3
Alberto Nuñez Feijoo
Alberto Nuñez FeijooHoto: Jesús Hellín/EUROPA PRESS/dpa/picture alliance

Yanzu haka Alberto Nunez  yana ci gaba da zawarcin jam'iyyun siyasar domin samun amincewarsu dan samun rinjaye domin kafa gwamnati. Daga cikin jamiyyun siyasar da yake kokarin zawarci har da ta 'yan yankin Kataloniya, wadanda suka kafa hujjar cewar za su bashi goyon baya ne kawai, idan ya amince ya yi afuwa ga yan fafutukar samun yanci kai 'yan Kataloniya da ake tsare da su tun a shekara ta 2017. Sai dai Alberto Nunez da  magoya bayan jam'iyyar ta 'yan mazan jiya, sun yi watsi da bukatun 'yan Kataloniyar. Kimanin 'yan Kasar ta Spain dubu 40,000 ne suka gudanar da zanga-zaga domin  yin tir da bukatun 'yan Kataloniyar:

Masu yin zanga-zangar adawa da yi wa 'yan Kataloniya ahuwa
Masu yin zanga-zangar adawa da yi wa 'yan Kataloniya ahuwaHoto: Susana Vera/REUTERS