1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma ya yi kiran zaman lafiya a Nijar

August 20, 2023

Shugaban darikar Katolika na duniya, Fafaroma Francis ya bukaci yin amfani da hanyoyi na diflomasiyya wajen warware rikicin siyasar Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulki da sojiji suka yi a kasar.

https://p.dw.com/p/4VNT5
Portugal | Weltjugendtag Heilige Messe Papst Franziskus
Hoto: Marco Bertorello/AFP

Fafaroma Francis ya nuna damuwarsa kan halin da ake ciki a Nijar kana ya bi sahun malamai wajen yin kiran wanzar da zaman lafiya a kasar da ma yankin Sahel baki daya.

Shugaban na Katolika mai shekaru 86, ya ce yana fatan kasashen duniya da ke shiga tsakani za su samar da mafita ta zaman lafiya nan ba da jimawa ba, wanda zai kasance alheri ga kowa.

A ranar 26 ga watan Juli ne dai, sojoji a Nijar din suka hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum, inda a yanzu kasar ke zama ta hudu da take karkashin mulkin soji a yankin yammacin Afirka tun daga shekarar 2020.