1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila: 'Yan sanda sun kai sumame a Al-Aqasa

Abdourahamane Hassane
April 5, 2023

'Yan sandan a Isra'ila sun kame mutane fiye da 350 a lokacin wani kazamin fadan da ya barke a masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus.

https://p.dw.com/p/4PjOj
Israel | Die Zusammenstöße in Jerusalem
Hoto: Ammar Awad/REUTERS

Fadan da aka yi a kan gwagwarmayar da aka dade ana yi ta mallakar masalacin na birnin Kudus tsakanin Falasdinu da Israi'la ya faru ne a daidai lokacin da Musulmi suke tsakiyar yin azumi na watan Ramadan,yayin da Yahudawan ke shirin gudanar da bukukuwan ista. Kasar Jordan da ke kula da wuraren tsarki na Musulmi a birnin Kudus, ta yi Allah-wadai da harin da aka kai a masallacin tare da yin kira ga sojojin Isra'ila da su gaggauta janyewa, yayin da Saudiyya ta yi watsi da matakin da ta ce ya sabawa ka'idojin kasa da kasa na jibge yan sanda a cikin wurin ibadar: