EU: Za ta taimaka wa 'yan gudun hijira a Girka
July 27, 2017Talla
Sabon tsarin wanda za a kashe kudade har Euro miliyan 209 kamar yadda babban kwamishina kungiyar ya bayyana zai taimaka wajen kyautata halin rayuwar masu neman mafaka. Wadanda ya ce a maimakon sauke su a gidajan bai daya zai ba da damar a rika daukar musu gidajan haya tare da daukar dauwainiyar su ta abinci da magunguna.