EU za ta kara wa Koriya ta Arewa takunkumi
September 7, 2017Talla
Kantomar da ke kula da harkokin wajen ta Kungiyar EU din Federica Mogherini ce ta ambata hakan a watan zantawa da ta yi da manema labarai kan takun sakar da aka cigaba da samu tsakanin Arewa da makotanta musamman ma Koriya ta Kudu kan gwaje-gwajen makamai. Mogherini ta ce nan gaba a yau za ta tattauna da ministocin harkokin wajen EU din a Estoniya kan batun Koriya ta Arewa inda ta ke cewar za ta bada shawarar a karawa Arewan takunkumin karya tattalin arziki. Kantomar ta ce duniya na fuskantar barazana sakamakon dabi'ar Pyongyang kuma ba za a barta ta yi kafar ungulu ga sha'anin tsaro da zaman lafiyar da kasashen duniya ke cin moriya ba.