1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta yi wa jakadanta da ke Nijar kiranye

November 23, 2024

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta yi wa jakadanta a Nijar kiranye, saboda sabanin da ta samu da kasar kan tallafin jin kai bayan ambaliyar ruwa da kasar ta fuskanta.

https://p.dw.com/p/4nLjq
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani Hoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Kakakin kungiyar EU, ya bayyana rashin jin dadinsa game da sanarwar da fadar mulki ta Niamey ta fitar na yin tir da taimkon jin kai miliyan 1,3 da EU ta bai wa Nijar ba tare da fara sanar da ita ba. Hakan ne ya sanya kungiyar ta kira jakadanta da ke birnin Yamai domin ganawa da shi a birnin Brussels na kasar Beljiyam. 

Karin bayani:Shugabar tawagar dakarun EU ta fice daga Nijar 

NIjar ta nemi jin ba'asin yadda za a kasafta tallafin. Tun dai a shekarar 2023, bayan da sojoji suka yi juyin mulki, gwamnatin mulkin sojin kasar ke juya wa kasashen Turai baya ciki har da uwargijiyarta Faransa. Dangantakar diflomasiyya tsakanin Paris da Niamey tana ci gaba da tsami tun bayan da Janar Tiani ya hambaar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum.