1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta yabawa yan sandan Jamus a G20

July 10, 2017

'Yan sandan Jamus sun taka rawar gani wajen shawo kan tarzoma a taron G20 a Hamburg a cewar shugaban hukumar tarayyar turai Jean-Claude Juncker

https://p.dw.com/p/2gHlv
G20 Gipfel in Hamburg | Polizei
Yan sandan Jamus cikin shirin ko ta kwanaHoto: Reuters/P. Kopczynski

Shugaban hukumar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker a yau Litinin ya kare matakin da yan sandan Jamus suka dauka a yayin zanga zangar lumana da ta rikide zuwa tarzoma a taron kungiyar kasashe ashirin masu cigaban masana#antu na duniya da aka kammala a birnin Hamburg a nan Jamus.

A cikin wata sanarwa Juncker yace rashin adalci ne sukar lamirin da ake yi wa yan sanda akan yadda suka tunkari lamarin.

Yace yan sanda sun sadaukar da rayuwarsu a wannan aiki mawuyaci, yana mai cewa sun cancanci yabo ne amma ba suka ba.