Martanin EU ga tattalin arzikin Turai
April 10, 2020Ministocin sun cimma yarjejeniyar amincewa da tsabar kudi euro biliyan 500 domin tallafawa kasashen bayan tsawon makonni suna tattaunawa kan illar da annobar cutar coronavirus ta yi ga tattalin arzikin kasashen.
Shugaban rukunin kasashen masu amfani da kudin na Euro Mario Centano yace daukar matakin cikin hanzari ya zama wajibi idan aka yi la'akari da irin halin da aka shiga a baya shekaru goma da suka wuce lokacin da kasashen duniya ciki har da nahiyar turai suka fuskanci koma bayan tattalin arziki.
"Yace wannan shirin agajin gaggawar zai bada kariya ga tattalin arzikinmu da sha'anin jin dadin jama'armu da kuma walwalarsu yayin da muka fuskanci koma bayan tattalin arziki. Idan matsalar da ake ciki ta lafiya kau, za mu bukaci farfadowar tattalin arziki a saboda haka yana da muhimmanci mu hada kai mu cigaba baki daya."