Takaddama tsakanin EU da Birtaniya kan haraji
April 2, 2019Sai dai kungiyar ta EU ba ta bayyana adadin kudaden da Birtaniya za ta karba, haka kuma ta ki ta bayyana kamfonin da abin ya shafa, to amma kuma ta bayyana cewa hukumomin Birtaniya su suke da alhakin bayyana kamfanonin da abin zai shafa dama iya adadin kudaden da kamfanonin za su biya.
Da take mayar da martani game da batun ma'aiakatar kudin kasar ta Birtaniya ta ce za ta gudanar da kyakyawan nazari kan batun kafin daukar duk wasu matakai. Matakin Kungugiyar na zuw ane a daidaii lokacin da ake cikin yanayi na rashin tabbas game da ficewar Birtaniya da yarjejeniya ko a akasin haka daga kungiyar.
A ranar 26 gha watan Oktoban da ya gabata ne hukumomin Tarayyar Turai suka kafa wani kwamitin bincike a daidai lokacin da ake cikin tattaunawar ficewar Birtaniya daga Kungiyar ta Tarayyar Turai.