EU na son dakile bakin haure daga tushe
May 18, 2017Kungiyar ta EU dai na wani sabon kokari na ganin ta sanya birki ga bakin haure da ma 'yan gudun hijira da ke biyo wa ta kasashen Libiya da ma Jamhuriyyar Nijar da ke zaman hanyoyi da 'yan gudun hijirar ke bi da nufin isa Turai. A cewar ministan harkokin cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere batun ba wai zai tsaya ga rarraba 'yan gudun hijirar ba ne da ke neman mafakar siyasa, har ma da fidda sabbin tsare-tsare da hadin kai wajen dakile matsaloli da ke addabar kasashen na Turai. De Maiziere da takwaransa na Italiya Marco Minniti dai a baya-bayan nan sun bayyana amannar cewa dole kasashen su tashi tsaye domin kare dubban daruruwa na rayukan mutane da masu fataucin mutane ke kasada da su su ratsa Libiya da Tekun Bahar Rum, inda sau da dama kwale-kwalen da suke amfani da su kan tuntsure su kuma nutse da mutane masu yawa, sakamakon rashin inganci.
Samar da rundunar tsaron EU a Afirka
Matakin dai kungiyar ta EU ke ganin zai taimaka, shi ne na samar da rundunar tsaro ta EU a tsakanin kasashen Libiya da Jamhuriyar Nijar ta yadda za su taimaka wa kasashe a kokarin rage kwarar bakin haure da 'yan gudun hijirar da ke son zuwa Turai, a kan haka ne ma ministan harkokin cikin gida da tsaro na tsibirin Malta, kasar da ke shugabancin kungiyar ta EU a yanzu haka, Carmelo Abela ya ce tuni ma sun fara tattaunawa da gwamnatin kasar ta Libiya, musamman kan batu na bayar da horo ga sojojin da ke aiki a gabar teku. Shi ma dai kwamishina mai kula da 'yan gudun hijira a Kungiyar ta EU Dimitris Avramopoulos bayyana bukatar da ke akwai ta samun gwamnatin hadin kan kasa a Libiyan ya yi domin su samu damar yin aikin hadakar cikin kwanciyar hankali. A taron na Brussels dai sun ma tattauna batun ka'idar adadin 'yaan gudun hijira da ko wacce kasa ya kamata ta dauka da ma kudin da za su rika fitar wa domin aikin da ya shafi 'yan gudun hijira da ma jin ko akwai sabbin tsare-tsare daga sabuwar gwamnatin Faransa karkashin Emmanuel Macron, koda yake a cewar ministan cikin gida na Jamus De Maiziere a koda yaushe Faransan da Jamus na kan matsaya guda ne.