EU na nazarin martanin haraji kan Amirka
October 4, 2019Jami'an kungiyar tarayyar Turai sun fada a yau Juma'a cewa suna fatan tattaunawa da Amirka kan sabbin kudin fito da ta kakaba kan kayayyakin Turai. Sai dai sun ce su ma a shirye suke su mayar da martani da karin haraji akan kayayyakin Amirka idan bukatar hakan ta taso.
Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas wanda ya baiyana hakan yace gwamnatin Amirka ta dauki hanyar fito na fito bayan da gwamnatin Trump ta sanya haraji mai yawa akan kayyakin tarayyar Turai.
Amirkar dai ta yi karin fiton ne bayan samun amincewar kungiyar ciniki ta duniya WTO akan rangwamen da tarayyar Turan ta ke yiwa kamfanin kera jiragen sama na Airbus.
Ita ma kungiyar tarayyar Turan ta ce ta na jiran hukunci kan rangwamen da Amirka ke yiwa kamfanin kera jiragen sama na Boeing wanda zai bata damar dora haraji akan kayayyakin Amirka.