1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Sahel uku ne ke fuskantar karancin cimaka

October 20, 2020

Majalisar Dinkin Duniya hadin guiwa da kungiyar Tarayyar Turai za su tallafa wa kasashen uku a yanki Sahel domin dakile matsalar karancin cimaka.

https://p.dw.com/p/3kCdS
EU AU Sahel Konferenz in Brüssel Mogherini mit Mahamat, Issoufou und Lacroix hold a joint news conference after an international High-Level Conference on Sahel in Brussels
Hoto: Reuters/E. Vidal

A wani taron da kasashen Jamus da Denmark suka jagoranta, karkashin kungiyar Tarayyar Turai gami da Majalissar Dinkin Duniya, ya sanar bayar da tallafin Euro miliyan43 ga kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso domin tsamosu daga  fadawa cikin kangin karancin cimaka.

Mai magana da yawun kungiyar ta Tarayyar Turai Balazs Ujvari ya ce an ware Euro miliyan 23 domin gudanar da ayyukan jin kai a kasashen, inda kuma za a yi amfani da Euro miliyan 20 wajen yaki da yunwa.

A wajen taron an bayyana kasashen uku a matsayin wadanda suka fi ko wace kasa a yankin Sahel fuskantar barazanar afkwa cikin karancin cimaka, sakamakon sauyin yanayi da karuwar al'umma.

Yara da dama ne dai taron ya ce basu samun damar zuwa makaranta. Wasu alkaluman kididdiga sun yi nuni da cewa mutane sama da miliyan 13 ne ke bukatar agajin gaggawa a iyakokin kasashen guda uku.