Taron kolin EU da China a Beijing
December 5, 2023China na fatan bunkasa dangantaka da kungiyar tarayyar turai a taron kolin da ke tafe tsakanin bangarorin biyu wanda zai mayar da hankali kan karfafa kawance bisa la'akari da kalubale mai sarkakakiya da ya dabaibaye dangantakar ta su a cewar ministan harkokin wajen kasar Wang Yi.
A taron da suka gudanar a Beijin da jakadun kungiyar tarayyar Turai da suka ziyarci China, Wang ya ce ya kamata bangarorin biyu su kalli dangantakarsu ta mahanga ta musamman yana mai cewa manufar China ga tarayyar turai ta na nan cikin lumana.
Kamfanin dillancin labaran Xinhua ya ruwaito Wang na cewa China da tarayyar turai na da ra'ayoyi mabambanta a kan al'amuran duniya da wasu bautuwa da suka shafi yankuna, sai dai ta hanyar tuntubar juna da kuma hadin kai ne kawai za su taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya tare da magance kalubalen da suka addabi duniyar.
Kalaman na zuwa ne gabanin taron koli da aka dade ana dako wanda za a yi a ranar alhamis tsakanin shugaban China Xi Jinping da shugaban majalisar Turai Charles Michel da kuma shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von de Leyen.